Ibrahim Magu yayi bayani ne alokacin da yake karbar muzaharar nuna goyon baya da wasu dubban yan kungiyoyi masu zaman kansu, kuma masu goyon bayan yaki da cin hanci da rashawa da suka kai ofishin hukumar EFCC a Abuja.
Inda yace wasu lauyoyi suna karbar makurdan kudade daga hannun ‘yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da ake yiwa shari’ar zargin satar dukiyar al’umma. Magu yace, “Wannan lauyoyi basu da aiki sai jiran wani yaje ya zalinci jama’a ya kwaso biliyoyin jama’a, wanda ya kamata ayi amfani da su wajen gina makaranta da Asibitoci da hanyoyi, amma sai an kama mutun sai suje su kawowa hukumar cikas….”
Yanzu haka dai akwai wani babban lauya guda daya da hukumar ta EFCC ta gurfanar gaban kuliya da laifin hana su gudanar da aikin
Shugaban hukumar EFCC, ya ci gaba da bayanin yadda ire-iren wadannan lauyoyi a baya suka sami tallafin gwamnati wajen samun damar yin karatunsu har suka zama mutane, amma yanzu suna hana ruwa gudu domin suna hana hukumar EFCC yin aikin ta. Amma Magu yace ba zai yarda da haka ba, zai yi duk abinda ya kamata wajen ganin an ja musu birki.
Domin Karin Bayani.