Hukumomin tsaro a jihar Kano sunce suna daukar matakan magance matsalar kwacen waya a hannu Jama’a da wasu batagarin matasa keyi a wasu sassa na birnin. A hannu guda kuma sana harkokin tsaro a Najeriya sun fara bada shawara ga sabuwar gwamnatin kasar dake tafe game da hanyoyin kawo karshen kalubalen tsaro a kasar.
Sai dai a ‘yan kwanakin nan wannan matsala tayi kamari, inda batagarin matasa kan yi fashin wayoyin hannun Jama’a masu tafiya a kasa ko kuma wadanda ke kan ababen hawa.
Malam Rabiu Ahmad, wani dan Jarida ya yiwa wakilin Muryar Amurka Mahmud Ibrahim Kwari bayanin yadda wasu batagari suka so raba shi da tasa wayar.”ina cikin mota a kusa da shatale-talen Isyaka Rabiu dake daura da Beirut Road kawai sai wani matashi ya zo bakin kofar mota ya ce da ni na taka shi da tayar mota, yayin da na leka na ce da shi ni ban taka shi ba, ashe su biyu ne abokin tafiyar tasa na daya bangaren ya zura hannun sa ya dauke min waya. Sai mutane suke ankarar da ni cewa, sun dauke maka waya fa. Nan take na kashe mota na bi su da gudu kuma na karbo waya ta kana na hada shi da ‘yan sanda”.
Sai dai hukumomin tsaro a jihar ta Kano sunce wannan sabon kalubale nada alaka ta kud-da-kud da ta’ammali da ababen sanya maye da matasan keyi.
Abubakar Idris Ahamd shine kwamandan shiyyar Kano na hukumar NDLEA, ya mai hana sha da fataucin ababen sanya Maye a Najeriya, yace wadannan batagarin matasa na amfani da ababen sanya maye kafin ko kuma bayan sun kwace wayoyi a hannun mutane , a don haka sai ya samar da runduna ta musamman a ofishin hukumar sa domin dakile wannan dabi’a.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da masana harkokin tsaro a Najeriya ke bayyana hanyoyi ko matakan daya kamata sabon shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dauka domin magance kalubalen tsaro a kasar bayan an rantsar dashi.
Manjo Mohammed Lawan Elyakub kenan mai ritaya, ya kawo shawarar cewa, shugaban Najeriya mai jiran gado yayi garanbawul a rundunar sojojin kasar data sama domin danka amanar yaki da kalubalen tsaro a hannun sahihan Jami’ai.
Abin jira a gani dai shi ne ko irin wadannan shawarwari ka iya tasiri ko akasin haka, musamman la’akari da yadda ‘yan Najeriya ke korafin cewa, ba kasafai shugabannin a kasar ke aiki da shawarwarin kwararru ba.
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari: