Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Ta'addancin Da Aka Kai Kenya


Wasu daga cikin kaburburan wadanda harin al-Shabab ya rutsa da su a Kenya
Wasu daga cikin kaburburan wadanda harin al-Shabab ya rutsa da su a Kenya

Ana cigaba da zakulo gawarwaki da kuma farautar 'yan ta'addan al-Shabab a Kenya

Sojojin Kenya da masu binciken halitta mai nasaba da wani abin da ya faru, wato 'forensic,' na cigaba da nemo karin gawarwaki a rukunin shagunan kasa da kasa na Westgate da ke Kenya, inda mamayar kwanaki hudu da wasu 'yan bindiga su ka yi ta kai ga mutuwar mutane sama da 65.

Masu nemo gawarwakin na kare hanci saboda wari a yayin da su ke kwakule-kwakulen rukunin shagunan da ya dan ruguje. wasu rukunonin sojojin kuma na binciken duk wata tarkon da mai yiwuwa an dana ko kuma 'yan bindigar da watakila har yanzu su na labe.

Hukumar Red Cross Shiyyar Kenya ta fadi jiya Laraba cewa har yanzu ba a san inda mutane sama 70 su ke ba.

Kungiyar 'yan bindigar al-Shabab ta Kenya mai alaka da al-Qa'ida ta ce ita ta kai harin na Westgate, wanda wani babban rukunin shaguna ne na alatu da 'yan kasashen waje da masu yawon bude ido da kuma attajiran Kenya kan so zuwa.

A halin da ake ciki kuma rahotanni daga arewa maso gabashin Kenya na cewa wasu maharan da ba a san ko su waye ba, sun tayar da bama-bamai a garin Wajir.

Hukumar Red Cross Shiyyar Kenya ta fadi a shafinta na Twitter cewa wasu tagwayen fashe-fashe da zafafan musayar muta sun bararraka garin na Wajir da yammacin jiya Laraba, agogo yankin.

Wata jaridar kasar ta Kenya, mai suna The Standard, ta ce maharan sun bude wuta yayin da su ke wuce wata Majami'a, su ka raunata mutane uku sannan su ka jefa abubuwan da ake kyautata zaton bama-bamai ne.

Jaridar ta ruwaito wani jami'in yansandar wurin na cewa jami'an tsaro sun shawo kan lamarin kuma su na kokarin farauto 'yan bindigar.

Wajir dai na wuri mai tazarar kilomita 500 ne daga arewa maso gabashin Nairobi, daura da kan iyakar Kenya da Somaliya.

Wannan harin ya zo ne kwanaki hudu bayan da kungiyar 'yan bindigar al-Shabab da ke Somaliya ta kai hari a rukunin shagunan Nairobi, inda su ka kashe mutane sama da 65.
XS
SM
MD
LG