Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin Kunar Bakin Wake Ya Hallaka Mutane Uku a Afghanistan


Wani wuri da aka kai harin bam a Afghanistan
Wani wuri da aka kai harin bam a Afghanistan

Akalla mutane uku suka mutu, kana wasu 20 kuma suka jikkata, a yau Laraba, sakamakon wani hari da aka kai a birnin Jalalabad da ke gabashin Afghanistan.

Rahotanni daga birnin Jalalabad na Afghanistan na cewa mutane uku sun mutu sannan wasu da dama kuma suka jikkata sanadiyar wani harin kunar bakin wake da aka kai.

An kai harin ne a ofishin kungiyar nan mai kula da yara ta Save The Children.

Atullah Khogyani, wanda shi ne kakakin gwamnati a gundumar Nanghahar, ya ce ayarin maharan sun afka ne cikin harabar ofishin, bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwasa motar da yake ciki.

Jami'an tsaro sun yi musayar wuta na wani lokaci mai tsawo da 'yan bindigar kamin a kawo karshen harin.

Sai dai Khogyani ya ce yanzu haka jami'an tsaro sun killace wurin jim kadan da kai wannan harin.

Sayed Ahmed wanda ya shaida lamarin, ya ce ya ga lokacin da wata mota kirar Toyota ta dunfari kofar da aka kai wannan harin.

Sannan jim kadan sai ya ji karar tashin bam, daga baya kuma sai wasu mutane uku zuwa hudu cikin kayan sarki suka shiga cikin ginin.

A cikin sakonta, kungiyar Save The Children, ta fitar da sanarwa ta shafin Twitter, inda ta ce tsaro, musamman ga ma'aikanta shi ne babban kalubalenta wajen gduanar da ayyukanta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG