Jami’an kasar sun ce harin ya kai ga ‘yan sanda, sun harbe wasu mutane biyu, sannan dukkanin wadanda suka raunata babu masu yawan shakatawa a cikinsu.
Wajen Ibadan, wanda ke birnin Luxor, na daya daga cikin wuraren da hukumar adana tarihi ta Majalisar Dinkin Duniya ta UNESCO ta ware, wanda wuri ne da ke jan hankulan masu yawan shakatawa na ciki da wajen kasar ta Masar.
Ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.
A ‘yan shekarun nan, masu kaifin kishin Islama, sun sha kai hare-haren bindiga da na bama-bamai a yankin Sinai da ke Masar, inda suka fi mai da hankali kan jami’an tsaro
Wadannan hare-hare, sun yi kamari ne, tun bayan da babban hafsan sojin kasar kuma shugaba mai ci a yanzu, Abdel Fatah Al Sisi, ya jagoranci hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Muhammed Morsi a shekarar 2013.