Litinin din nan za'a fara taron koli na kasashe masu arzkin masan'antu a Jamus.
Shugaban Amukr da sauran shugabanni kasashe da suke cikin wannan kungiya tuni suka isa wajen taron.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana halartar wannan taro bisa gayyatar da shugabanni dake cikin wannan kungiya suka yi masa.
Sai dai tafiyarsa ba ko wani dan Najeriya ne yake goyon bayansa ba. Alhaji Abdulkadiri Balarabe Musa, yana cikin wadanda suke ganin bai kamata ace shugaban yana hulda da shugabannin kasashen da har yanzu suke neman su ci gaba da yiwa kasashe kamar Najeriya mulkin mallaka.
Alhaji Balarabe Musa, yace mafi da cewa yanzu shine shugaba Buhari ya maida hankali wajen hada kan Najeriya, da kuma gyara tattalin arziki. Sannan daga bisani ya fara hulda da irin wadannan kasashe.
Amma kakakin jam'iyyar APC Alhaji Lai Mohammed yace, halartar wannan taro yana da muhimmancin gaske, domin idan ma akwai wata manufa, zuwa taron ne zai bada damar a gane abunda suke kullawa.
Ga karin bayani.