Wasu mahara su uku sun kai harin da ya kashe mutane fiye da 40 a filin jirgin saman Ataturk na Istnabul a Turkiyya, daya daga cikin filayen jiragen saman da suka fi cika da jama'a a fadin duniya.
Harin Kunar-Bakin Wake A Filin Jirgin Saman Istanbul

5
Layin karbar takardar shiga jirgi wayam babu kowa a cikin filin jirgin saman Istanbul Ataturk.

6
Jirage su na shawagi a kasa a filin jirgin saman Istanbul Ataturk, Laraba 29 Yuni 2016.

7
Wasu mutane su na gaida junansu a jikin wata tutar Turkiyya da kuma mutumin da ya kafa sabuwar kasar ta zamani, Mustafa Kemal Ataturk, a filin jirgin saman Istanbul Ataturk a bayan harin bam na jiya talata.

8
Fasinjoji su na jiran shiga filin jirgin saman Istanbul Ataturk a bayan harin bam na jiya talata.