Wasu mahara su uku sun kai harin da ya kashe mutane fiye da 40 a filin jirgin saman Ataturk na Istnabul a Turkiyya, daya daga cikin filayen jiragen saman da suka fi cika da jama'a a fadin duniya.
Harin Kunar-Bakin Wake A Filin Jirgin Saman Istanbul

9
Iyalan wata mai suna Gulsen Bahadir, wadda ta mutu a harin bam na filin jirgin saman Istanbul Ataturk a jikin makarar dake dauke da gawarta lokacin da aka yi jana'izarta yau Laraba, 29 Yuni 2016 a Istanbul.

10
An sauko da tutar Turkiyya kasa kasa a filin jirgin sama mafi girma na Turkiyya, Istanbul Ataturk, bayan harin ta'addancin da aka kai can jiya talata