A karo na biyu Ministan Shari’ar kasar, Abubakar Malami ya ki bayyana a gaban kwamitin kula da harkar shari’a na majalisar dattawa domin su binciki gurfanar da shugabannin majalisar da aka yi a farkon makon nan.
Koda ya ke Fadar shugaban kasar ta tura wani wakili a madadin ministan, to amma kuma sai aka fatattakeshi daga Majalisar da cewa, su Mai Shari’a Abubakar Malami suke bukata ba Mashawarcin Shugaban kasa a game da harkar shari’a ba.
Mista Obula ya fusata kwarai bayan fatattakar da aka yi masa, inda ya cewa wakiliyarmu ta Muryar Amurka a Majalisa Madina Dauda jawabi cikin fushi da cewa kawai sun so yankwana su ne bisa takama da majalisa.
Shima daya daga cikin ‘yan Majalisa Joshua Ludani ya bayyana matsayar da kwamitinsa ke ciki da kuma dalilin da yasa aka bukaci Ministan Shari’ar ya hallara a gabansu game da shari’ar shugaban Majalisar Abubakar Bukola Saraki.