Hukumomin Afghanistan sun ce mayakan kungiyar Taliban sun ta da bam a wata mota da ke makare da ababan fashewa a kusa da ofishin hukumar leken asirin kasar da ke tsakiyar gabashin birnin Ghazni.
A yau Lahadi Kakakin ma’aikatar lafiyar kasar, Mohammad Hemat, ya tabbatar da mutuwar mutum 12, ciki har da fararen hula, kana wasu sama da 180 sun jikkata.
“Ya zuwa yanzu, mun kwantar da mutum 88 a asibiti, wadanda suka ji raunuka a wurin harin bam din, 27 daga cikinsu kananan yara ne, wadanda shekarunsu ba su wuce tsakanin 8 zuwa 10, sannan daga cikin wadanda suka mutu akwai dan karamin yaro daya.” Inji shi ne shugaban ma’aikatar lafiya a birnin na Ghazni, Zaher Shah Niklam,.
Tuni dai kungiyar ta Taliban, ta dauki alhakin wannan hari, wanda ta ce ya lalata ginin hukumar tsaron kasar da ake kira NDS a takaice, tare da jikkata mutane da dama.