Rundunar saman sojin Najeriya ta yi ikrarin kashe wasu shugabannin kungiyar ‘yan ta’adda na ISWAP a yankunan Jubillaram da Alinwa da ke arewacin jihar Borno a Najeriya.
Darektan yada labaran rundunar, Air Commodore Ibikunle Daramola, ya bayyana hakan a Abuja a jiya Asabar, inda ya ce, rundunar tsaro ta “Operation Lafiya Dole” tare da hadin gwiwar “Operation Rattle Snake III” sun kai farmaki akan shugabannin kungiyar.
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin tsaro a Jamhuriyar Nijar da ke makwabtaka da Najeriyar su ma suka yi ikrarin cewa dakarun kasar sun halaka ‘yan ta’adda sama da 100.
A Najeriya an kai hare-haren saman ne a daidai lokacin da shugabannin ke kungiyar ta ISWAP ke shirin yin wani taro a cewar Daramalo kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a yau Lahadi.
Shafin yanar gizo na gidan talbijin din TVC a Najeriya, shi ma ya ruwaito Daramola yana cewa an kashe "kusoshin kungiyar" ta ISWAP da dama.
Sai dai sanarwar ta Daramola, ba ta ambaci adadin shugabannin kungiyar ta ISWAP da aka kashe ba ko mukamansu a kungiyar.
A Jamhuriyar Nijar, ma’aikatar tsaron kasar ta ce ta sami nasarori sosai a rawar dajin da aka kaddamar a farkon watan nan na Fabrairu, tare da hadin gwiwar sojojin rundunar Barkhane a Arewacin yankin Tilabery da iyakar Mali da kasar.
Sojojin Nijar da takwarorinsu na Faransa sun kaddamar da rawar daji ne a arewacin yankin Tilabery da kan iyakar Mali da kasar, a ranar 1 ga watan Fabrairu.
Hukumomin tsaron kamar yadda wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Souley Moumouni Barmah ya rawaito sun kuma kama kimanin babura 10 hade da wasu kayayyakin hada bama-bamai hadin gida.
Dakarun Nijar da dama suka rasa rayukansu a ‘yan watannin bayanan, sanadiyyar hare-haren da ake kai w akan barikin sojojin kasar.
Wadannan hare-hare a kasashen biyu da ke fama da matsalar ‘yan ta’adda na faruwa ne a daidai lokacin da ake korafin jami’an tsaro ba sa tabuka komai, musamman a Nijar da ke dauke da dakarun kasashen wajen da dama musamman na Faransa.
Jama'a da dama a Nijar, sun yi ta korafin a janye dakarun Faransa saboda a cewarsu ba su da amfani, bukatar da hukumomin kasar suka amince wa da ita.
A Najeriya ma, an yi ta kiraye-kirayen Shugaba Muhammadu Buhari da ya sauke manyan shugabannin tsaron kasar, bayan da kungiyar Boko Haram ta zafafa kai hare-hare, baya ga matsalar satar mutane da ta addabi sassan kasar.
Amma gwamnatinsa ta ce akwai matakan da ake bi kafin a sauke shugabannin tsaron.
A baya-bayan nan, kungiyar ta Boko Haram ta kai hare-hare a wasu yankunan jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe, an kuma rasa rayuka da dukiyoyi da dama.
Saurari rahoton Souley Moumouni Barmah daga Yamai: