Kasar Rasha da take kai hari a kasar Syria wadda yaki ya daidaita ta fada ya'u laraba cewa tayi amfani da jiragen yaki na ruwa guda hudu ne a tekun CASPIAN domin kaddamar hari na musammam a wannan kasar.
Ministan Tsaro na kasar ta Rasha Sergei Shoigu ya fadawa shugaba Vladirmin Puttin cewa jirgin ya cilla rokoki damisalin karfe 11 ga kungiyar ISIL kuma yayi musu kaca-kaca ba tare da yashafi farar hula ba ko guda.
Shoigu Yace sakamakon wannam harin ya tabbatar da cewa wannan roka yana da faida kwarai da gaske domin ko yana kaiwa nisan kilomita dubu daya da dari biyar cikin dan kankanin lokaci.
Rasha dai tana kai wannan harin ne ta ruwa a kasar ta Syria bayan da ta daddale tsakanin ta Amurka da Turkiyya cewa zasu yi aikin hadin gwiwa a wannan wuri.