A cikin sanarwa da kungiyar ta wallafa a internet, ISIS tace ta kaddamar da harin kunar bakin wake hudu akan kuradun gwamnatin, wanda bayanan da ta bayar suka saba wa abund a jami'an gwamnati suka bayar cewa, an kai hare haren ne har da rokoki da 'yan tawayen kungiyar Houthi da suke samun goyon bayan kasar Iran.
Hadaddiyar daular Larabawa ta fada jiya Talata cewa,harin da aka kai a Aden ya kashe sojoji 15, ciki harda sojojin Yemen da dakarun kasar Saudiyya wacce take yiwa rundunar taron dangin jagora.
Kamfanin dillancin labarai na daular da ake kira WAM a takaice ya zargi 'yan tawayen Houthi da kai harin, 'yan tawayen da yanzu fiye da shekara daya suke fafatawa da gwamnatin kasar. Hadaddiyar daular Larabawan tana cikin runduar taron dangin da kasar Saudiyya take yiwa jagoranci.
A gefe daya kuma, akalla mutane shida ne suka mutu sakamakon wata fashewa kusa da wani masallaci a Sana'a babban birnin kasar.