Dr Ahmed Dukawa na jami’ar Bayero Kano, ya bayyana dambarwar siysar da ta dabaibaye Majalisar Dokokin Tarayyar Najeriya a matsayin babban abin takaici, da kyama da kuma ban mamaki. Kasancewa jam’iyar da ta hau karagar mulki ta hanyar zabe, ta nuna a fili cewa, bata so ta kyale ‘yan majalisa su zabi shugabanninsu ta hanyar zabe.
Dr Dukawa ya bayyana cewa, jam’iyar APC ta bayyana karara cewa, so take tayi nadi ba zabe ba, duk da yake tana ikirarin cewa, jam’iya ce mai neman ganin an yi adalcil, wanda bisa ga cewarshi ba daidai bane a tsarin damokaradiya. Yace damokaradiyar cikin gida da ake Magana a kai ta ce, sai dukan ‘ya’yan jam’yar sun amince da dukan wadansu mukamai a yisu ta hanyar zabe, kuma duk wani wanda za a tsayar takara, a yishi ta hanyar zabe, kuma dukan wanda ‘yan majalisa zasu zaba a matsayin shugaba, a yi shi ta hanyar zabe, to a nan ake damokaradiyar cikin gida, amma wannan da suke nuna cewa, wane shine wane, to wannan ba damokaradiya bace, sun nuna cewa nadi ne suke so su yi wanda wannan , tawaya ce a tsarin damokaradiya.
Dangane kuma da ba hammata iska da ‘yan majalisar suka yi, Dr Abati yace, bai kamata su bari a kai ga haka ba, ganin irin yanayin da kasar ke ciki da kuma yanayin da jam’iyarsu ta APC ke ciki, kasancewa mutane suna ganin APC tamkar kishiyar PDP, saboda haka ba a zaci zasu tsaya suna bata lokaci a kan batun raba mukamai ba.
A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa Mahmud Ibrahim Kwari, Dr Dukawa yace mafita kawai ita ce, APC ta koma tsarin damokaradiya, idan ba haka ba, zata yi ta asarar membobi. Bisa ga cewarshi, abinda kawai ya kamata tayi shine ta amince da duk zabin da ‘yan majalisa suka yi.
Ga cikakkiyar hirar: