Harin na Madina ya faru ne a wani shingen biciken abababan hawa da ke wajen daya daga cikin muhimman wurare na Musulmi.
Miliyoyin Musulmi ne su ke halartar wannan wuri a duk shekara a lokacin aikin hajji.
Ministan aikace-aikacen cikin gida, ya ce maharin ya ta da bam din ne bayan da wasu jami’an tsaro suka tunkare shi.
A jiya Litinin, masallacin ya kasanae cike makil da jama’a, yayin da ake shirye shiryen bikin sallah karama.
Duk da harin da aka kai, kafofoin yada labaran Saudiyya sun nuna hotunan jama’a suna ci gaba da tururuwa zuwa masallacin.
Har ya zuwa yanzu babu wanda ya dauki alhakin kai wannan hari.
Hukumomin na Saudiya har ila yau na ci gaba da binciken wani harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin ‘yan Shi’a a gabashin birnin Qatif, inda ministan cikin gidan ya ce an gano wasu sassan jikin mutane uku, amma ba a gane ko su wanenene ba.