Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce, har sai al’umar kasar musamman masu hanu da shuni, sun nuna hali na sadaukar wa kafin kasa ta ci gaba.
“A halin da Najeriya ke ciki yanzu, akwai bukatar kowa da kowa ya nuna hali na sadaukar wa idan har muna so mu magance matsalolin cin hanci da talauci da aikata manyan laifuka da kuma rashin ci gaban da muke fuskanta.” Inji shugaba Buhari.
Buhari ya bayyana hakan ne, yayin da yake ganawa da wasu shugabannin jihar Katsina a Daura, kamar yadda wata sanarwa da mai bai wa shugaba Buhari shawara kan harkar yada labarai, Malam Garba Shehu, ya saka wa hannu wacce Muryar Amurka ta samu.
Sanarwar ta kara da cewa, shugaba Buhari ya jaddada cewa “akwai lokutan da dole sai al’umar kasa ta sadaukar da rayuwa ta jin dadi” kafin kasa ta ci gaba.
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari ne ya jagoranci tawagar shugabannin jihar zuwa Birnin na Daura, domin su yi wa Buhari ta'aziyyar bisa rashin wasu ‘yan uwansa da aka yi.
Facebook Forum