Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KADUNA: Nakasassu Sun yi Gungu Kan Dokar Hana Barace barace


 Nasir El-Rufai gwamnan jihar Kaduna
Nasir El-Rufai gwamnan jihar Kaduna

Kimanin wata daya ke nan da sabuwar gwamnatin jihar Kaduna ta fito da wasu sabbin tsare tsare da suka hada da haramta barace barace da tallace tallace da yansu wasu suka fara tustu da su.

Tsari na baya bayan nan shi ne hana barace barace a gefen hanya da tallace tallace.

To amma wasu da abun ya shafa sun ce sam dokar ba zata taba zama karbuwa ba a wurinsu saboda ta wannan hanya ce kadai suke ciyar da kansu da iyalansu da kuma samun biyan bukata..

Ranar Asabar da ta wuce nakasassu a Kaduna sun yi gungu domin nuna rashin jin dadinsu game da dokar suna cewa babu gudu babu ja da baya daga barace baracen da suke yi. Malam Muntari Sale mai magana da yawun kungiyar nakasassu ta jihar Kaduna yace gwamna El-Rufai ya sa ana kamasu ba tare da basu abincin da zasu ci ba ko aikin da zasu.

Malam Muntari Sale ya rantse da Allah cewa ba zasu bar barace barace a Kaduna ba sai dai idan za'a hallakasu gaba daya.

To saidai gwamnatin jihar tace duk da tirjewar nakasassu matsayin gwamnati kokarin tsarkake tsaron jihar ne da samun tsarin da zai anfani kowa. Samuel Aruwa mai magana da yawun gwamnatin jihar ya sake jaddada dalilin hana barace barace da tallace tallace. Yace harakar tsaro ta sa gwamnati daukan matakin. Sun yi hakan ne domin tsaurara matakan tsaro da kuma kare rayukan mutane..

Ga rahoton Isa Lawal Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG