BIRNIN N’KONNI, NIGER - Hukumomin na Nijar, sun fitar da sanarwar sayar da farashin kudin na hajjin bana a lokacin wata ganawa da dukkan masu ruwa da tsaki a ayyukan aikin na Hajji, musamman hukumar shirya aikin Alhazai ta kasa KOHO.
Malam Saidu Usman ministan kasuwanci na Jamhuriyar Nijar ya ce abokan huldar mu akan wannan maganar ta aikin hajji, sun yi mana kallo da idanun basira, game da kiraye-kirayen da hukumomin wannan kasar suka yi, tun daga shugaban majalisar koli ta soja dake mulkin wannan kasar, ya zuwa Firai Ministan Lamine Zeine, don kai ga farashi mai sauki ga al'ummar wannan kasar na neman tafiya ibada kasa mai tsarki da ya kai sama da sefa miliya uku.
Wannan ya nuna cewa a kara godiya ga Allah, kuma kowa ya gane cewa, dole ne, ya sa nasa kokari domin cimma wannan buri .
A cewar magatakardan kungiyar ma'aikatan CDTN reshen Birni N'Konni, Alhadji Idrissa, wannan farashi yayi, duk da yake, in har za a iya samu, suna bukatar a kara ragewa.
Wannan tsayar da farashin kudaden kujerar aikin hajjin na wannan shekara ta 2024, ya wanzu ne bayan wata ziyarar aiki da hukumar ta aikin hajji ta yi a kasa mai tsarki tare da ganawa da hukumomin Saudiya, inda ma hukumar ta bada sanarwar wadansu kudade dake nasaba da irin wahalhalun da alhazan Nijar suka sha a bara, ta rashin samun wadansu ababe da ke kasancewa hakkokin su ne a cikin aikin hajji, abinda ya sa ma ministan kasuwancin na Nijar jan hankullan masu ruwa da tsaki a kan ayyukan aikin na hajjin bana.
Saurari cikakken rahoto daga Haruna Mamman Bako:
Dandalin Mu Tattauna