Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

HAJJ 2024: Wadansu Ma’aurata Daga Jihar Maryland Na Daga Cikin Wadanda Suka Mutu A Makka


Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie
Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie

Wadansu ma’aurata daga Bowie, jihar Maryland na daga cikin sama da mutane dubu daya da suka rasu sakamakon matsanancin zafi yayin aikin hajjin bana a kasar Saudiya.

Alieu Wurie dan shekaru 71 da matar shi Isatu Wurie ‘yar shekaru 65 sun dade suna burin zuwa aikin hajji tare, amma burin nasu bai cika ba sai bana.

A bayaninta, ‘yar su, Saida Wurie tace a sako na karshe da ta samu daga mahaifiyarta ta bayyana cewa, ita da mahaifinta sun yi tafiya ta tsawon sa’oi biyu a cikin matsanancin zafi, kuma tun daga wannan lokacin ba a sake jin daga gare su ba, washegari abokan tafiyar da suke tawaga daya da iyayen suka shaida mata cewa, sun wuce sa’oi 24 ba su dawo otel ba kuma su kadai ne su ka bace a tawagar ta kusan mutane 80.

Alieu Dausy da Isatu Wurie
Alieu Dausy da Isatu Wurie

Bayan kwanaki biyu wani daga cikin tagawar ya kira ya shaida masu cewa, an sami sunayen iyayen nata, tare da lambar takardun fasfo dinsu a jerin sunayen wadanda suka mutu sakamakon matsanancin zafi, an kuma yi jana’izarsu.

Saida ta bayyana cewa, iyayenta sun yi kyakkyawan shiri gabanin tafiya aikin hajjin da ya hada da sayen ruwa da za a kara masu a jiki idan ta kama, da kuma yin tafiya mai tsawo a cikin unguwa na tsawon watanni kafin lokacin tafiyar, domin su saba.

Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie
Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie

Alieu da Isatu Wurie sun san juna tun suna kananan yara domin uwayensu kawaye ne. Sun yi aure a shekara ta 1983 amma suka rabu bayan shekaru goma, suka kuma sake yin aure a watan Disambar bara, bayan shekaru 13 da mutuwar aurensu.

Jami'an gwamnati da 'yan siyasa a Karamar Hukumar Prince Georges na jihar Maryland, sun aika da sakonnin taya iyalin jajen rasuwar ma'auratan.

Angela Alsobrooks Shugabar Karamar Hukumar Prince Georges kuma 'yar takarar Majalisar Dattijai karkashin tutar jam'iyar Democrat ta wallafa a shafinta na X cewa,"Ni da tawagata mun sami wasu munanan labarai a yau. Wasu masoyan kungiyar #TeamAlsobrooks guda biyu, Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie, sun rasu a yayin da suke gudanar da aikin hajjin bana a Makka sakamakon tsananin zafi. Haja Isatu Wurie ta kasance mai kwazo a cikin al'ummarmu. Ta shiga cikin kungiyoyin al'umma da yawa, da su ke tasiri a cikin al'ummar mu da duniya baki daya. Ina mika gaisuwar ta'aziya ta ga da iyalansu a wannan mawuyacin lokaci. An yi babban rashi, kuma za a yi matukar kewarsu."

Ita ma a nata sakon ta’aziyar, ‘yar kansila a karamar hukumar Prince Georges Wala Blegay Blegay ta bayyana cewa ta fara saduwa da Isatu Wurie wadda ta kasance daya daga cikin jiga-jigan al’ummar Musulmi a karamar hukumar lokacin da ta shiga takarar neman kujerar kansila a Karamar Hukumar, ta ce, Haja Wurie taimaka mata gaya wajen fahimtar kalubale da Musulmi da ke da yawa a karamar hukumar su ke fuskanta, ta kuma bada gagaruwar gudummuwa a yakin neman zaben da ya kai ta ga nasara a 2022.

Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie
Alhaji Alieu Dausy da Haja Isatu Wurie

Alieu da Isatu Wurie sun rasu sun bar ‘ya’ya uku, Mohammed mai shekaru 40; Alieu, dan shekara 39; da kuma Saida Wurie ‘yar shekaru 33, da jikoki hudu.

Kafin rasuwarsu, Alieu Wurie yana zama galibi a kasar shi Saliyo inda ya ke aiki a ma’aikatar ilimi, yayinda Isatu ta yi ritaya bara, bayan shafe shekaru 30 tana aiki da daya daga cikin mayan kamfanonin inshorar lafiya a Amurka da ake kira Kaiser Permanente.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG