Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwannatin Nijer Na Kokarin Magance Kalubalen Ruwan Sha A Kasar


A Jamhuriyar Nijer, cinkoson jama’a a manyan birane wanda ya samo asali daga karuwar yawan al’umar kasar ya haddasa karancin ruwan sha, lamarin da ya sa gwamnatiin kasar ta soma daukar matakai domin magance wannan matsalar.

Wannan matsalar ta ruwan sha wani batu ne dake kara ta’azzara a ‘yan shekarun nan a birane da karkara duk kuwa da irin matakan da hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu ke dauka lamarin da masana ke dangantawa da karuwar yawan al’uma a wani lokaci da ake fama da matsalar wutar lantarki, a cewar Habou koure Jakou, darektan ma’aikatar kula da albarkatun ruwa a matakin birane.

Rashin tattali da nuna halin ko in kula na daga cikin matsalolin da aka gano cewa suna haddasa karancin ruwa a birane inji Ousman Dambaji shugaban kungiyar REJEA mai kare hakkin jama’a a fannin ruwa da tsafta.

Ministan albarkatun Ruwa, Farfesa Issouhou Katambe ya bayyana cewa tuni gwamnati ta fara hangen bullo da matakan da zasu bada damar sassauta wahalhalun jama’a a fannin ruwan sha.

Samar da tsari musamman game da farashin ruwan sha tsakanin attajirai ko manyan ma’aikata masu karamin karfi na daga cikin hanyoyin da gwamnatin Nijer ke hange don karfafa matakan samar da wadatar ruwa, abinda ya sa a baya bayanan majalisar dokokin kasar ta amincewa shirin kafa hukumar zuba ido akan harkokin ruwan sha.

Saurari cikakken rahoton wakilin Murya Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG