Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnonin Kudu Maso Gabas Sun Jaddada Aniyar Inganta Tsaro a Yankin


'Yan bindigar kudu maso gabashin Najeriya.
'Yan bindigar kudu maso gabashin Najeriya.

Gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya sun sake jaddada aniyyar inganta matakan tsaro, domin magance fitintinun da kan addabi sassa na yankin da ma na kasar baki daya.

Mista Emmanuel Uzor ne mai magana da yawun gwamnan jihar Ebonyi Injiniya Dave Umahi, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin kudu maso gabas. Ya dai bayyana muhimmancin kafa cibiyar tsaro a yankin a wata hira da Muryar Amurka.

Ya ce, "Kowa na sane da halin da tsaro ke ciki a kasar, kuma kowane yanki na matukar shirin tsare al'ummarsa, ciki har da yankin kudu maso gabas. Saboda haka, abin da gwamnonin yankin suka yi shine su amince akan wani samfurin tsaro da cewa ya kamata a kafa rundunar tsaron dazuka, ya yin da kowace jiha na iya kafa nata rundunar. Ba 'yan sanda bane, kuma ba zasu rika yawo da makamai ba. Aikinsu shine tattara bayanan sirri akan bata-gari. Zasu kuma rika bai wa jami'an tsaro bayanai akan abubuwan da na iya tada zaune tsaye. Sun amince kuma da kafa cibiyar tsaro a Inugu, da zata rika karbar bayanai akan yanayin tsaro a jihohin yankin."

Wannan lamarin dai ya samar da yabo daga wasu masu ruwa da tsaki a yankin, cikin har da shugaban kungiyar matasan kabilar Igbo, Mazi Okechukwu Isiguzoro.

Wanda ke cewa "Muna yaba wa gwamnonin kudu maso gabas bisa wannan matakin, saboda alhaki ya rataya akansu ne su tsare rayuka da dukiyoyi, da kuma dakile wasu miyagun laifuka kamar garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a duk fadin yankin. Ya kamata gwamnonin Arewacin kasar da na kudu maso yamma da kuma na kudu maso kudu su kwaikwayi wannan. Idan kuwa suka yi hakan, zasu kara taimaka wa kokarin gwamnatin tarayya wajen kawo karshen rikice-rikicen da suka mamaye sassa daban-daban na kasar."

A nasa ra'ayin kuma, wani malamin jami'a, Mista Ugochukwu Ogbonnaya ya ce yana lale marhabin da wannan ci gaba.

"Ina marhabin lale da wannan lamarin da ya kamata a ce an aiwatar dasu tun da jimawa. Gwamnoni sune shugabannin tsaro na jihohinsu, kuma sun san matakan da suka fi dacewa wajen kare rayuka da dukiyoyi a jihohinsu. Ina ganin wannan zai taimaka sosai wajen kare kowa da kowa, da masu gari da kuma mazauna. Banda wannan, wadannan matakan za su kara karfafa kokarin gwamnatin tarayya na shawo kan matsalar rashin tsaro," inji Mista Ugochukwu.

Shi kuma Dakta Celestine Nwosu mai fashin baki kan lamuran yau da kullum cewa ya yi, "Ina tunanin cewa ba laifi bane gwamnonin suyi hakan domin su kare al'ummominsu, saboda matukar basu yi hakan ba, za a ci gaba da samun aukuwar miyagun laifuka. Saboda haka, daukar wadannan matakan na da kyau, muddin zasu yi komai bisa tanadin doka."

A ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnonin kudu maso gabashin Najeriya suka gudanar da wani muhimmin taro a Inugu, babban birnin Jihar Inugu, inda suka tattauna akan batun samar da tsaro mai dorewa a duk fadin yankin.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Alphonsus Okoroigwe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG