Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Najeriya Na Bukace Da Tsarin Tattara Sakamakon Zabe Ta Yanar Gizo - Tambuwal


Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.
Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal.

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, ya yi kira ga majalisar dokokin Najeriya da ta tabbatar da dokar amfani da na’ura wajen tattarawa da aikewa da sakamakon zabe a tsarin zaben kasar.

A yayin da yake jawabi ga manema labarai a Sokoto, Gwamnan Tambuwal, wanda kuma tsohon kakakin majalisar wakilan Najeriya ne, ya shawarci ‘yan majalisar dokoki na tarayya da su maida hankali kan bukatun jama’ar da suke wakilta, ba ra’ayin wasu daidaikun shugabanni ba.

Tambuwal ya bayyana yakinin cewa ra’ayin dukkan ‘yan kasa ne a samar da doka wadda za ta tabbatar da sahihin tsarin zabe a Najeriya.

Zancen kudurin dokar yin garambawul ga tsarin zaben kasar dai na ci gaba da janyo cece-kuce, tun sa’adda aka ba da rahoton cewa ‘yan majalisar sun cire shedarar da ta ce za’a yi amfani da na’orori wajen tattarawa da aikewa da sakamakon zabe daga cikin sabon kudurin.

‘Yan majalisar da dama sun kafa hujja da cewa amfani da na’urar zamani a tsarin zaben kasar ba zai yiwu ba saboda rashin ayukan sadarwar yanar gizo wato ‘internet’ a yankuna da dama na karkara a kasar.

Karin bayani akan: Gwamnan Tambuwal, jihar Sokoto, Nigeria, da Najeriya.

To sai da Gwamnan Tambuwal ya ce hukumar zabe ta INEC ta tabbatar da cewa tana da kayan aikin na zamani da za ta iya tattarawa da aikewa da sakamakon zabe ko da kuwa babu yanar gizo.

“Dalilin wannan, kamata yayi a bai wa hukumar zaben ta INEC damar soma amfani da tsarin zabe da na’urorin zamani, tun da har ta ce za ta iya” in ji gwamna Tambuwal.

Ya kara da cewa “wannan zai ba da damar kowa na iya ganin sakamakon zabe ba tare da wata matsala ko kuskure ba da zara an sanar da shi tun daga cibiyar tattara sakamako. Kuma INEC ta tabbatar da cewa idan aka yi amfani da tsarin, to kowane dan Najeriya da ke bukata, na iya bibiyar yadda tsarin zabe da sakamakon zaben ke tafiya daga cikin gidansa.”

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal Ya Yi Kiran Amfani Da Tsarin Tattara Sakamakon Zabe Ta Yanar Gizo A Najeriya

Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal Ya Yi Kiran Amfani Da Tsarin Tattara Sakamakon Zabe Ta Yanar Gizo A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:41 0:00

Gwamnan Tambuwal ya ba da misali da zabukan gwamna biyu da hukumar zaben ta gudanar kwanan nan tare da gwajin amfani da na’urorin zamani da ya ce sun kayatar sosai, inda PDP ta lashe na jihar Edo, yayin da APC ta yi nasara a jihar Ondo.

A Najeriyar dai an jima ana hankoro tare da fatan ganin zuwan lokacin da za’a soma amfani da fasahar zamani wajen tsarin gudanar da zabuka a kasar, sakamakon dogon tarihin ayukan tafka magudi da aringizo da suka dabaibayin tsarin.

Majalisar dokokin kasar ta yi kokarin gyara kan sashe na 50 sakin layi na 2 na daftarin kudurin yin garambawul ga tsarin zabe na shekarar 2021, domin shafe tanadin tattarawa da aikewa da sakamakon zabe ta yanar gizo, lamarin da kuma ke ci gaba da haifar da cece-kuce da ra’ayoyi daban-daban daga ‘yan Najeriya.

XS
SM
MD
LG