Gwamantoci a duniya sun sha alwashin farautar zakakuran masu kudi da masu mulkin da ke bude boyayyun asusun ajiya a kasashen ketare don boye dukiya da kuma gujewa biyan haraji. Wannan ya biyo bayan rahoton da kungiyar wasu ‘yan jaridar duniya suka fitar ne.
Wanda suka fallasa cewa, sun gano mutane na fakewa da bude wasu kamfanoni a wasu kasashen da sunaye daban-daban don aikata almundahana, kamar yadda wata Maggie Murphy daga wata Kungiyar yaki da rashawa Transparency International ta bayyana.
An dai bayyana cewa an sami wasu dimbin takardu daga wani Kamfanin Lauyoyin da ake kira Mossack Fonseca da suka nuna alakar wasu hada-hadar shige da ficen kudin na kusan shekaru 40 daga Rasha zuwa Panama, wanda haka ke da alaka da Shugaba Vladamir Puttin to daga shekarar 1977 zuwa ta 2015.
Tuni dai gwamnatin Kremlin ta yi fatali da wannan rahoton da ta ce kawai kai tsaye ya soki shugaba Putin ne. Musamman ma da aka ce wasu tsoffin jami’an Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka da na Hukumar leken asiri ta CIA ne suka taimaka wajen nazarin takardun hada-hadar.