Wannan kuwa ya biyo bayan wani sumame ne da hadakar kungiyar Fulani ta Tabital Puulaku Njonde-Jam suka kai a wani yankin Maiha dake kan iyakan Najeriya da Kamaru.
Wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul’aziz, ya ziyarci yanki dake karamar hukumar Maiha, akan iyakar Najeriya da Kamaru. inda har ya tarar da yan kungiyar Tabital Puulaku sun cafke wani da ake zargin shine malamin barayin. Wanda ya rantse da cewa shi bai san mutumin da yake yiwa aiki barawo bane.
Bayan haka kuma dubun wasu barayin Shanu da kuma Fulani masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ya cika domin kugiyar Tabital Puulaku ce ta cafke su.
Wani mazaunin wannan yanki yace a kwanakin baya an kama masa yaransa har hudu, inda ya biya kudi sama da Naira Miliyan hudu kafin a sake su.
Shugaban kungiyar Tabital Puulaku, Alhaji Abdu Bale, yace dalilinsu na shiga wannan yanki shine yadda wasu mutane suka kame ya yan Fulani domin neman kudin fansa, hakan ne yasa mutanen yankin suka gayyaci wannan kungiya. Yanzu haka dai bayan zuwan wannan kungiyar mutanen sun saki yara sama da goma suka kuma gudu, ba tare da an biya su ko sisin kwabo ba.