Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Trump Ba Ta Shirin Tsawaita Dokar Ba da Tazara


Gwamnatin Trump ba ta shirin tsawaita dokar yin nesa-nesa da juna da gwamnatin tarayya saboda cutar coronavirus, daga yau Alhamis da dokar za ta kare aiki, a maimakon haka tana maida hankali ne akan kokarin aiki tare da jihohi a kan shirye-shiryen sake bude kasar.

Gwamnonin jihohi ke yanke shawarar yaushe za’a sassauta dokar rufe kasuwancin shaguna marasa muhimmaci a jihohinsu, da haduwar jama’a da yawa, da kuma umarnin ci gaba da zama a gida.

Shugaba Trump ya fada a jiya Laraba cewa, ka’idojin gwamnatin tarayya da aka kafa tun a tsakiyar watan Maris za su kau sannu a hankali, yayin da gwamantinsa ta ke tuntubar gwamnoni domin jin nasu shirye-shiryen.

Jami’an kiwon lafiya sun yi gargadi a kan yunkurin Trump na gaggauta bude al’amura, suna cewa yin hakan zai iya haddasa sake dawowar kamuwa da cutar.

Adadin wadanda suka kamu da Covid-19 a duniya ya kai miliyan 3.2 a yau Alhamis, yayin da yawan wadanda suka mutu ya haura dubu 227,000, a cewar kididdigar jami’ar Johns Hopkins.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG