Fitaccen likitan nan na Amurka da ya kware kan cututtuka masu yaduwa, Dr. Anthony Fauci, ya ce ya ga alama akwai fa’ida a tattare da maganin nan na Remdesivir wajen jinyar cutar COVID-19.
Da ya ke magana a lokacin wata ganawa da Shugaban Amurka Donald Trump da sauran mambobin kwamitin yaki da cutar coronavirus, Fauci ya ce wani binciken da aka yi kan maganin na Remdesivir ya nuna cewa maganin na iya kare mutane daga coronavirus.
Fauci ya ce sakamakon binciken bai nuna cewa maganin na iya hallaka cutar kwata-kwata ba, to amma ya nuna cewa akwai kwakkwarar alamar fa’ida a maganin.
Fauci ya kara da cewa maganin na Remdesivir ya dan taimaka wajen rage mace-mace, saboda kashi 11% na majiyatan ba su sha wannan maganin ba ne suka mutu, a yayin da kuma kashi 8% na wadanda su ka sha su ka mutu.
Facebook Forum