WASHINGTON, DC —
Kalamun da gwamnan jihar Borno yayi kan sojojin Najeriya ya sa gwamnatin tarayya mayarda martani.
Doyin Okupe mai taimakawa shugaba Jonathan kan harkokin jama'a yace babu yadda za'a ce sojojin Najeriya basu da kayan aiki ko kuma 'yan tsageran Boko Haram sun fisu kayan aiki. Yace babu yadda zaka iya tunkarar sojojin Najeriya domin haka yana mamakin har wani yace 'yan ta'ada sun fisu kayan aiki.Okupe yana mayarda martanin gwamanatin tarayya ne kan kalamun gwamna Kashim Shettima na jihar Borno.
Shi ma Nasiru Zaharadeen mai taimakawa shugaban kan hulda da jama'a yace gwamna Shettima ba soja ba ne har da zai san irin kayan aikin da sojoji ke dasu a jihar Borno kuma ba abu ba ne da ita gwamnatin tarayya zata shiga gidan radiyo tana bayyana irin makaman da sojojinta suka mallaka ba. To sai dai ba'a iya farma 'yan ta'adan da manya mayan makamai ba domin wasu da basu ji basu gani ba za'a rutsa da su.
Dangane da rashin kai sojoji kowane kauye musamman a jihohin dake karkashi dokar ta baci Nasiru Zaharadeen yace hakan ba zai yiwu ba domin wuraren nada yawa. Yace yaki ne na sari ka noke inda wani lokaci 'yan tsageran na hadewa da mutane ko kuma su sanya kayan soji.
To sai dai shugaban kungiyar Izala Sheik Bala Lau yace akwai bukatar hadin kan 'yan Najeriya domin kalubalantar sha'anin matsalar tsaro a kasar. Yace garin Izhige an kai hari kan Musulmi da Kirista. Masu wannan ta'adancin suna yi ne kan masu bin addinan biyu saboda haka suna kawo ma zaman lafiya ne barazana. Idan babu zaman lafiya da Musulmi da Kirista babu wanda zai iya yin addinisa. Yace lamarin yayi muni harma matan aure ne suka yiwa mazajensu sallar jana'iza.
Dangane da kafa wani zaure tsakanin shugabannin addinan biyu Sheikh Bala Lau yace taron da suka yi a Legas sun bada shawara a jawabin karshen taro cewa a nemi wata majalasi ko wani inuwa da za'a zauna tsakanin Musulmi da Kirista domin idan babu Najeriya tamkar babu mu gaba daya ne. Tun da Allah Ya riga ya hada mu wuri guda sai mu yi hakuri da juna.