WASHINGTON, DC —
Tuni wasu al-ummomi dake kunshi da mutane fiye da dubu a yankin suka kauracewa gidajensu zuwa shedkwatar karamar hukumar, yayinda har yanzu ba’a san inda wasu suka shiga ba.
Wannan dai na zuwa ne yayinda ake cigaba da jimamin kwanton baunan da wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojoji a yankin Izge, yayin da sojojin ke kan hanyar kai ceto.
Da yake tabbatar da halin da al-umman kan iyakar ke ciki da kuma kwanton baunan da aka yi wa sojojin, daya daga cikin shuwagabannin karamar hukumar Madagali, Mr. Maina Uluramo yace ‘yan bindiga sun tarwatsa al-ummomi da dama, saboda haka ne suke kiran a kafa rundunana musamman a yankin.
Mr. Maina yace “an kawo zuwa Izge, to su kuma mutanen Izge suna guduwa zuwa Madagali. Muna kiran gwamnati ta dauki mataki akan wannan abun, a san yanda za’a yi tsare wannan waje inda mutane suke”.