Wasu majiyoyi da mutanen garin sun ce an kashe mutanen da suka zarce hamsin a wannan farmakin, amma kuma ba a ji ta bakin sojoji ko gwamnatin jihar Adamawa kan wannan adadin ba.
Mazauna kauyen suka ce a cikin dare wadannan 'yan bindiga, wadanda ake kyautata zaton 'yan kungiyar na ta Boko Haram ce, suka far ma kauyen inda suka yi ta yanka mutane tare da harbi.
An ce mutane da dama sun tsere suka bar kauyen cikin dare.
Kauiyen na Izghe da kuma yankin karamar hukumar Madagali a jihar ta Adamawa, suna iyaka da wani makeken dajin dake cikin jihohin Borno da Yobe da Adamawa, inda a nan ne ake kyautata zaton 'yan Boko Haram suke da sansanoni.
Dukkan garuruwan da ake kai ma hari, kamar Benisheikh, Maiduguri, Konduga, Bama, Gwoza, Damboa, Madagali, su na kewaye da wannan dajin ne.