Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Rikon Kwaryar Nijar Ta Sallami Shugaban Hukumar ‘Yan Sanda Akan Wasu Kalamai


Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
Sojojin da suka yi juyin mulki a Jamhuriyar Nijar

Gwamnatin rikon kwaryar Jamhuriyar Nijar ta tsige Shugaban hukumar ‘yan sandan birnin Yamai kwanaki kadan bayan da ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda wasu daga cikin masu zanga-zangar nuna bukatar ficewar sojan Faransa ke wuce gona da iri har ma da yin fatali da doka.

NIAMEY, NIGER - Da hantsin wannan Litinin 11 ga watan Satumba ne takardar tsige Shugaban ‘yan sandan birnin Yamai Contoler General Abdoulsalam Mahaman dauke da sa hannun Ministan cikin gida General Mohamed Toumba ta fara karade kafafen sada zumunta, wacce wata majiyar sabbin hukumomin na Nijar ta tabbatar wa Muryar Amurka da sahihancinta.

Abin tuni a ranar Larabar da ta gabata ne Shugaban hukumar ‘yan sandan birnin Yamai Abdoulsalam Mahaman ya gargadi masu zaman darshan a harabar sansanin sojan Faransa da ke dab da filin jirgin saman Yamai da su koma gefen titi domin bai wa masu ababen hawa damar kai da kawo ba tare da wata tsangwamaba.

Ya kuma nuna rashin jin dadinsa akan yadda wasu daga cikin wadanan mutane ke uzurawa masu ababen hawa da suke tilasta cire belt ga masu motoci ko hular kwano ga masu babura.

Controler General Abdousalam a wannan rana ya sanar cewa, suna da bayanan cin zarafin mutane a wannan wuri ciki kuwa har da yi wa mata fyade saboda haka ya bukaci hadin kan jagororin zanga-zangar domin tabbatar da doka da oda.

Ba a dai yi bayani a hukunce kan dalilan daukan wannan mataki ba, to amma a ra’ayin wani dan farar hula na gamayyar Reseau Esperance Bachar Maman za ta yiwu abin na da nasaba da furicin da Shugaban ‘yan sandan na Yamai ya yi game da abubuwan da ke wakana a harabar Escadrille.

Da ma tun a ranar ziyarar ta Controler General Abdoulsalam daya daga cikin jagororin wannan zanga-zanga Gamatche Mahamadou ya rubuta a shafinsa na facebook cewa, kalaman na Shugaban ‘yan sandan birnin Yamai zagon kasa ne da ya kitsa takanas da nufin karfafa guiwa ga mukarabban tsofuwar gwamnati, saboda haka ake ganin rubutunsa tamkar shawara ce ya bai wa hukumomin mulkin soja.

Tun a washe garin juyin mulki na 26 ga watan Yuli ne matasa suka kaddamar da ayyukan binciken motoci da ababen hawa a titunan birnin Yamai, galibi da dare da nufin dakile yunkurin dukkan wata aika-aika.

Haka kuma irin wannan aiki ke gudana daga ran 1 ga watan Satumba a harabar sansanin sojan Faransa, sai dai wasu mazaunan birnin Yamai sun koka kan yadda wasu daga cikin masu aikin binciken ke wuce gona da iri, wasu ma na ganin tamkar masu zanga-zangar na shiga hurumin jami’an tsaro.

Saurari ciakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Gwamnatin Rikon Kwaryar Nijar Ta Sallami Shugaban Hukumar ‘Yan Sanda Akan Wasu Kalamai.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG