KEBBI, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da jama'ar yankunan suka soma nuna bajinta ta tsayawa su kare rayuka da dukiyoyinsu daga barayin daji.
Jama'ar yankunan kudancin jihar Kebbi sun jima suna fama da matsalolin 'yan bindiga musamman a garuruwan da ke kusa da yankin jihohin Naija da Zamfara.
Sau da yawa 'yan bindigra ke kai hari su kashe mutane ko su sace wasu a wadannan yankunan, yayin da wasu lokuta suma sukan sha wuya, kamar a harin da suka kai a wannan mako, inda jama'a suka fuskance su.
Shugaban karamar hukumar Danko Wasagu, Hussain Aliyu ya ce tun farko an samu labarin cewa barayin sun fito ne daga yankin jihar Naija.
Mutanen yankunan dai sun nuna farin ciki da samun wannan galaba, sai dai sun nuna bukatar kara mayar da hankali ga samar da tsaron yankunan baki daya.
A daidai lokacin hada wannan rahoto, wani mutumin yankin da aka kashe 'yan bindiga 17 ya shaida mana cewa suna zaman dar-dar domin koda yaushe akwai yuwuwar barayin su dawo yankin don mayar da Martani.
Masana lamuran tsaro dai sun jima suna bayar da shawarwarin yadda suke ganin za a iya samun saukin wannan matsala ta rashin tsaro a Najeriya yayin da su kuma mahukunta ke cewa suna kokarin shawo kan matsalar har ma suna samun nasarori, a lokaci daya kuma jama'ar yankunan da ke da matsalar sai kokawa suke yi akan yadda har yanzu suke fama.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna