A ranar Asabar kungiyar yan jaridun kasar Venezuela ta bayyana cewa, hukumomi a kasar sun saki wata yar jarida da aka zarga da ta’addanci, aka kuma kama ta bayan kammala sake zaben shugaba Nicolas Maduro mai cike da takaddama na watan Yuli.
Ana Carolina Guaita, da aka kama a ranar 2 ga watan Agusta, yar jarida ce ta La Patilla, wata kafar labarai dake yawan caccakar gwamnati.
Kungiyar ma’aikata yanjaridu ta kasar ta fada cikin wata wallafa a kafar sadarwar zamani, cewa, an tsare Ana a kurkuku na tsawon sama da watanni 4 a birnin La Guaira dake kusa da gabar ruwa, arewa da babban birnin kasar, Caracas.
Kungiyar tace, an zarge ta ne da ta’addanci, da tunzira jama’a da haifar da cikas a bisa hanyoyin da jama’a ke bi.
Kafin kamun na ta, Guaita ta dauko rahoto a lokacin da aka tintsiro da mutum mutumin marigayi shugaba Hugo Chaves, wanda Maduro ke ikirarin zama magajin Chaves, a yayin zanga zangar bayan zabe.
Bore dai ya barke a sassan kasar bayan da aka ayyana Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben ranar 28 ga watan Yuli, duk kuwa da sakamakon zaben da bangaren adawa suka wallafa da ya nuna dan takarar su ne ya lashe zaben da gagarumin rinjaye.
Boren ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 27, da raunata wasu 200, aka kuma kama mutane har 2,400.
Kasashe kalilan ne da suka hada da kawayen Venezuelan na kud da kud irin su Rasha suka amince da sake zaben Maduro a karo na 3 na zagayen shugabancin shekaru 6.
Sakin na Guaita ya zo ne sa’oi bayan hukumomi sun sanar da sakin tsararru 200.
Bisa lissafin gwamnati, mutane 733 ne aka sako daga jarun, duk da dai kungiyar kare hakkin bil’adama ta Foro Penal tace, hakikanin gaskiyar adadin mutanen da aka saka bai kai hakan ba.
Dandalin Mu Tattauna