Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan bayan ya yi wa ‘yan jarida bayani a fadar gwamnati a karshen zaman majalisar zartarwa ta tarayya ta yanar gizo.
Mohammed ya ce Gwamnatin Tarayya ta yi ta tattaunawa da dama da Twitter inda ya kara da cewa ana samun ci gaba.
Ya bayyana cewa za a janye dakatarwar da aka yi na shafin Twitter nan ba da jimawa ba.
Yace; "Mun bayyana abin da muke so daga Twitter. Ƙarshen ƙudurin tattaunawar sulhu ya kusa. ”
“Mun yaba da hakurin‘ yan Najeriya. Ina so in tabbatar muku cewa mun sami ci gaba sosai."
"Su (Twitter) sun nuna sassaucin ra'ayi sosai." Ya kuma kara da cewa duk da cewa Twitter ta amince da wannan sharadin, tana ci gaba da cewa kafa ofishinta zai iya kai wa 2022.
Idan ba a manta ba a ranar 5 ga Yuni, 2021, Gwamtin tarayyya ta hana Twitter aiki a hukumance har abada, bayan haka kuma ta hana kamfanin aiki a Najeriya bayan dandalin sada zumunta ya goge sakon twitan da Shugaban, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya) ya kafa a shafinsa game da 'yan kungiyar asalin Biafra (IPOB).
Gwamnatin tarayya ta fassara goge sakon twitan Buhari a matsayin rashin mutunci kuma ta danganta ta "da dimbin matsaloli da ke tattare da dandalin sada zumunta a Najeriya, inda labaran karya da na bogi suke yaduwa, abun da ke haifar da munanan tashe-tashe hankula a duniya".