Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Muktar Ramalan Yero a gaban kotu.
Wata sanarwa da EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce an gurfanar da Yero ne a gaban babban kotun mai Shari’a R.M. Aikawa a Kaduna da ke arewacin Najeriya a ranar Litinin.
Ana tuhumar shi kan wasu laifuka takwas da aka sabunta, wadanda suka danganci halalta kudaden haram a cewar sanarwar.
Ana tuhumar tsohon gwamnan ne tare da wasu mutane uku, wadanda suka hada da Nuhu Somo Way, wanda tsohon minista ne da tsohon sakataren gwamnatin Kaduna Ishaq Hamsa, sai tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Gaiya Haruna.
Dukkansu ana tuhumarsu kan karba da raba kudi Naira miliyan 700 daga hannun tsohuwar ministar mai Diezani Alison-Madueke wacce ta ba su don su yi amfani da su a yakin neman zaben 2015, zargin da suka musanta.
An dage sauraron karar zuwa ranakun 16, 17 da 18 na watan Janairun 2023.