A wani taron manema labarai kwamishaniyar kiwon lafiya ta jihar Hajiya Hadiza Abdullahi ta bayyana inda cibiyoyin suke.
Tace sun ware wurare shida tun kafin ma cutar ta shigo jihar. A karamar hukumar Borgu sun ware guda daya. Akwai daya a Shiroro. Akwai daya kuma a Jaji cikin Mokwa.
Idan har lamura suka yi muni za'a bude daya a Kontagora, daya a Lahun daya kuma a Suleja. Gwamnati ta bada kwangilar sayen kayan sawa na musamman da ake bukata kafin a ga mai cutar ebola.
A halin da ake ciki majalisar limaman masallatan Juma'a da gwamnati tace zata nemi hadin kai da su domin sanin abun da ya kashe mutum kafin a yi masa jana'iza, sun bayyana matsayinsu akan lamarin. Imam Umar Faruk sakataren majalisar limaman yace a shariar musulunci ba'a yadda ba maiwanke gawa ya tabata da yatsunsa. Akwai abun da ake sawa kafin safar hannu ta roba ta fito. Yanzu da aka samu safar duk limamai masu wanke gawa sai sun yi anfani da safar hannun. Tantance gawa babu laifi idan an iya ganewa. Amma ba zasu yadda da kona gawar musulmi ba wai domin hana yaduwar cutar.
Ma'aikatar kiwon lafiya ta karyata wani rahoto dake cewa cutar ta shigo jihar ta Jamhuriyar Benin.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.