Wata sanarwa da Kwamishinan tsar on cikin gida Samuel Arwan ya wallafa a shafinsa na Twitter ta nuna cewa, an saka dokar ce a yankin Chikun da kuma kananan hukumomin da ke kudancin jihar.
“Wadannan yankuna sun hada da, Barnawa, Kakuri, da Television a kudancin Kaduna sannan sai Maraban Rido, Sabon Tasha, Narayi, Unguwan Romi da suke karamar hukumar Chikun.” Sakon Twitter ya nuna.
Sanarwar ta kuma yi Allah wadai da “da yunkurin tunzura mutane da ake yi a kafafen sada zumunta.”
“Gwamnati na kira ga daukacin al’uma da su yi watsi da tunzura su da ake yi, su kuma gujewa duk wani da zai haddasa rudani ya kuma kawar da doka da oda.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi da Aruwan, kwamishinan ya ce, “ba su waye suka kai far wajen ajiyar abincin ba.”
Ya kuma ce sun dauki matakin ne a matsyain kandakari don kada ya jirkice ya koma tarzoma.
Wannan lamari na faruwa ne a daidai lokacin da ake zanga zanga nuna kyamar rundunar tsaro ta SARS a wasu sassan kasar, yayin da boren ya jirkice y a koma tarzoma a yankunan Najeriya da dama.
Facebook Forum