Gwamnatin jihar Adamawa ta sanya dokar ta-baci a kan al'ummomin da rikicin ya barke a karamar hukumar Lamurde da ke jihar.
Wannan ya biyo bayan tashin hankalin da ya barke a Tingno, Dutse da Tito a ranakun Alhamis da Jumma’ar da suka gabata, tashin hankali da ya lakume rayuka fiye da talatin baya ga wadanda aka raunata da yanzu haka ke jinya a asibitin kwararru dake Yola dama wasu asibitocin.
Rahotanni sun ce ko a jiya Lahadi wasu majiyoyin kabilanci sun kashe wasu mata biyu da ke tafiya zuwa Lafiya Lamurde daga Tigno.
Gwamnatin jihar Adamawan dai tace kafa dokar hana fita na tsawon awanni 24 nan take, da nufin dakile harin sari ka noken da ake kaiwa a wasu yankunan karamar hukumomar Lamurden.
Mr. Solomon Kumangar daraktan yada labaran gwamnan jihar, yayi karin haske game da dokar hana fita da gwamnatin ta kafa, inda ya ce, kafa dokar zai taimaka wajen hana ci gaba ko yaduwar wannan rikicin zuwa wasu sassa. Sannan gwamnati tana binciken musabbabin faruwar rikicin. Kuma wadanda suka samu raunuka ko suka rasa muhallin su, gwamnati zata basu tallafi.
Ya zuwa yanzu rundunan ‘yan sandan jihar ta tabbatar da cafke mutum 30 game da rikicin na Tigno. DSP. Suleiman Yahya Nguroje kakakin rundunan ‘yan sandan jihar ya bayyana halin da ake ciki a yanzu. Inda ya ce, a binciken da ‘yan sanda suka yi sun samu nasarar kwace bindiga, da sauran makamai kamar su adda, wukake.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum