Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba da umurnin a kaddamar da wani farmakin soji na musamman domin magance matsalar ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane a jihar Katsina.
Wata sanarwa da mai taimakawa Buhari a fannin yada labarai Garba Shehu ya fitar Lahadi, ta nuna cewa “dakarun kasar na musamman sun fara wani shiri, wanda har yanzu ba a yi cikakken bayani a kansa ba.”
Shirin a cewar sanarwar, “zai dakile hare-haren da ake kai wa a sansanonin ‘yan gudun hijira.”
Domin kaddamar da wannan shiri, wata tawaga ta musamman ta isa jihar don tsara yadda za a aiwatar da wannan farmakin da “ba a taba ganin irinsa ba.”
Tuni dai babban hafsan soji mai kula da harkokin tsaro, Janar Olonisakin, ya yi wa shugaba Buhari bayani kan yadda yake sa ran za a gudanar da wannan shirin a cewar Shehu.
Shugaba Buhari wanda ya nuna baccin rai kan yawan hare-haren da ake kai wa a jihar, ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasu sanadiyyar hare-haren.
A ‘yan kwannakin nan, jihar ta Katsina na fuskantar karin hare-hare wadanda kan jawo asarar rayuka da dama.
Facebook Forum