Da alamar dai an yi asarar rayuka da dukiyoyi sanadiyyar wani tashn hankalin da ya barke a garin Tigno na Karamar Hukumar Lamurde a jahar Adamawa ta arewacin Najeriya.
'Yan garin sun ce fadan ya barke ne tsakanin Hausawa da Chobawa, a wannan garin, wanda akasari manoma ne. Shi dai wannan tashin hankalin ya soma tashi ne tun a shekaranjiya Alhamis sakamakon rikici a tsakanin wasu mutum biyu kan babur, to amma kuma sai lamarin ya kazance a jiya jumma’a, inda aka shiga kaiwa juna hari da kone kone, lamarin da ya jawo asarar rayuka da kuma dukiyoyi.
Tuni dai gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin jihar da kuma hukumomin tsaro zuwa garin na Tigno dake cikin karamar hukumar Lamurde, don duba halin da ake ciki inda ya bada umarnin da a kwashe yan gudun hijiran da rikicin ya shafa zuwa garin Lafiya Lamurde.
DSP Suleiman Yahya Nguroje kakakin Rundunan 'Yan sandan jihar ya ce kawo ayanzu ba a da adadin wadanda suka rasa rayukansu ko kuma wadanda rikicin ya shafa, kuma tuni aka kara tura jami’an kwantar da tarzoma zuwa yankin don maido da doka da oda ayanki.
Yankin Tigno dai wuri ne dake da albarkatun noma, musamman shinkafa,kuma akwai kyakkayawan zaman takewa a tsakanin al’ummun garin kafin faruwan wannan tashin hankali
Ga Ibrahim Abdul'aziz da cikakken rahoton:
Facebook Forum