Rahotanni sun sunan cewar hakan na faruwa ne a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke kira ga gwamnatin da ta yi maza-maza ta sake su, ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Amurka ma ta yi Allah wadai da lamarin, inda ta ce matakin tsare mutanen ya yi tsauri, ganin cewa sun fita ne suna zanga zangar lumana.
A ranar Asabar ne jami’an tsaro suka tsare shugaban babbar jam’iyar UDP Ousaini Darboe, tare da wasu masu goyon bayansu.
Akwai kuma bayanai da ke nuna cewa, Sakataren tsare-tsaren jam’iyar, Solo Sandeng ya rasa ransa sanadiyar azabtar da shi da aka yi.
Sai dai Ministan yada labaran kasar, Sheriff Bojan, ya ce bashi da wata masaniyar cewa wani da ya ke tsare ya mutu.
Amma kuma ya ce wadanda ake tsare da su, sun karya dokar da ta hana yin zanga zanga ba tare da izini ba.