Cikin ‘yan kwanakin nan anyi fama da tashin bama-bamai da ke da nasaba da rikicin Boko Haram, a Jahohin Borno da Adamawa. Tashin bam na baya bayan nan shine wanda ya faru a kasuwar garin Madagali, wanda wasu mata ‘yan kunar bakin wake suka tayar har yayi sanadiyar rayuka. Sai kuma tashin bam da aka samu a karshen makon nan a garin Maiduguri, wanda shima yayi sanadiyar asarar rayuka.
Wannan batu dai ya fara tayar da hankulan al’ummomin da suka fara komawa yankunansu da aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram.
A zantawarsa da Muryar Amurka, gwamnan jahar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ya nuna kaduwarsa game da abubuwan da suke faruwa, ya kuma ce bai kamata jama’a suki komawa garuruwansu ba.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin jahar Adamawa ta fara tunanin hana saka hijabi a wasu yankunan jahar, biyo bayan yawaitar samun hare haren kunar bakin wake.
Tun bayan fara rikicin Boko Haram a Najeriya, an sami asarar dubban rayukan mutanen da basu jiba basu gani ba, haka kuma rikicin ya raba Miliyoyin mutane da muhallansu da tilasta musa zama ‘yan gudun hijira.
Domin karin bayani.