Gwamnatin jahar Adamawa ta bakin kakakin ta Mallam Ahmed Sajoh ta maida martani game da kwamitin mutane bakwai da mukaddashin babban Jojin jahar Ambrose Mammadi ya kafa a ranar jumma'a domin binciken gwamna Murtala Nyako da mataimakin shi Bala James Ngillari wadanda majalisar dokokin jahar ke kokarin tsigewa bisa zargin su da dimbin laifuffuka masu alaka da tafiyar da mulkin jahar da kuma gudanar da baitalmali.
Kakakin gwamnatin jahar Adamawa Mallam Ahmed Sajoh ya ce ba a ma kafa kwamitin a kan k'aida ba ganin cewa a lahadin nan wa'adin babban Jojin ya kare.
Idan ba a manta ba dai majalisar dokokin jahar ce ta bukaci babbar kotun jahar Adamawa ta kafa kwamitin da zai binciki gwamna Murtala Nyako na jam'iyar APC da mataimakin shi Bala James Ngillari na PDP.
Wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya ce wata majiya mai tushe ta tabbatar da cewa wasu kusoshin jam'iyar PDP wadanda ke cikin masu son a tsige har da mataimakin gwamnan dan jam'iyar su, sun garzaya Abuja yanzu haka su na neman kar matakin tsigewar ya shafe shi.
A Tattaunawar su da wakilin mu Ibrahim Abdulaziz mataimakin gwamnan jahar Adamawa Bala James Ngillari ya ce tun farko ai da ma ba su yi mi shi adalci ba. Ya ce ya so su kira shi su saurari bayanan shi tukuna kafin su yanke hukunci, amma sam ya ce babu wanda ya neme shi. Sannan ya kammala da cewa idan mutum ya na aiki da gaskiya, komin dadewa gaskiya za ta yi halin ta.