Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Ta Fara Sauraren Kokenmu - Dillalan Man Fetur A Najeriya


Karancin man fetur a Najeriya, Mayu 26, 2015
Karancin man fetur a Najeriya, Mayu 26, 2015

Mai yiwuwa ana kusa da samun saukin matsalolin da kan haifar da karamcin man fetur a Najeriya, abin da sau da yawa ya kan jefa rayukan jama'a cikin kunci.

SOKOTO, NIGERIA - Wannan na zuwa ne lokacin da dillalan man fetur masu zaman kansu, suka ce gwamnati ta fara magance korafe-korafen su, wadanda rashin kulawa da su ne ke kai su shiga yajin aiki.

‘Yan Najeriya sun jima suna ganin tasko sanadiyyar ja-in-ja, tsakanin gwamnatin kasar da dillalan man fetur kan abin da ya shafi biyan kudin dakon mai, abin da wani lokaci yake kai su shiga yajin aiki har jama'a su galabaita.

Yanzu akwai alamun samun saukin wannan matsala da yake dillalan sun ce gwamnati ta fara sauraren kokensu da kunnuwan basira, kamar yadda shugaban kungiyar dillalan mai na Depo a Gusau, Sirajo Yahaya Kamba ya shaida VOA.

A cewar Kamba, watannin baya sun koka kan biyan kudaden dakon mai, saboda sun yi aikin da ya kamata a biya su, to wannan lokaci kuma an soma biyan su kudin, kan haka ne ma suke son jin ta bakin sauran dillalan in sun gamsu da biyan da aka soma.

Shugaban dillalan fetur a Sokoto, Usman Abubakar Randy, ya ce lallai sun gamsu da yadda biyan ya gudana, yana mai cewa, yanzu babu batun yajin aiki kuma babu maganar rufe gidajen mai saboda an saurari kokensu an fara biyan su hakkinsu, kuma suna kan kokarin ci gaba da samar da mai domin al'umma su amfana.

Sai dai wani abu mai kama da hanzari ba gudu ba, shi ne duk da yake masu biyan bashin kudin dakon sun soma gamsuwa da matakin da gwamnati ta fara dauka, ‘yan Najeriya ba su ga sauyi ba a gidajen man na ‘yan kasuwa.

Wakilin kwamitin amintattu na kungiyar dillalan man a Najeriya Muhammad M. Jega ya ce mutanen da ke kula da farashin Mai su kula da shi tun a depo domin can ne ake samun bambancin farashi domin ba ya yiwuwa dan kasuwa ya sayo mai ya fadi.

Masana tattalin arziki a Najeriya, sun jima suna tsokaci akan tallafin man fetur da gwamnatin kasar ke bayarwa har wasu na ganin janye shi ne kawai mafita.

Bashir Muhammad Achida na jami'ar Usmanu Danfodiyo na ganin cewa sauya fasalin kamfanin mai na kasa da gwamnati ta yi, wata hanya ce ta lalabo mafita ga matsalolin.

Masu lura da lamurran yau da kullum, na ganin cewa biyan bashin kudin dakon mai da gwamnatin ta soma, ana iya kallonsa ta fuskoki da dama, ciki har da karatowar lokacin zabe, gwamnatin take son magance matsalolin da ke yi wa ‘yan kasa tarnaki domin fuskantar zabe cikin sauki, tamkar abin da ke gudana yanzu a haujin samar da tsaro.

Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:

Gwamnati Ta Fara Sauraren Kokenmu - Dillalan Man Fetur A Najeriya .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:17 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG