Garba Muhammad Bindiga Karaye kwamishanan gona na jihar kuma shugaban kwamitin bunkasa noman shinkafa da alkama ya ce wannan manufa da aka shirya Allah ya sa an cimma nasara.
Ya ce burin shi ne a bunkasa kasa da abinci, jama'a su samu aiki kana tattalin arzikinsu ya karu sannan kudaden da ake fita da su sayo abinci su zama an ajiyesu ko kuma a mayar da su wani gefen a yi amfani da su.
A cikin ranin bana za 'a noma shinkafa wajen tan miliyan 2.5, sannan akwai manoma 3000 masu kadada guda guda da suka shiga aikin. hade da kuma manyan manoma wajen 3000.
Shugaban kungiyar masu noman shinkafa a jihar ta Kebbi ya bayyana irin tasirin da wannan shirin ya yi a fannin tattalin arziki inda ya ce suna noma yanzu kuma suna samun riba ba kaman da ba da suke faduwa.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna da karin bayani.
Facebook Forum