Alhaji Ibrahim Gaidam, yace gwamnatin sa bata taba karbar ko sisin kwabo ba daga wajen gwamnatin Tarayya, na tallafawa ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya dai dai ta. Gwamnan ya bayyana haka ne alokacin da yake rantsar da shugabannin kananan hukumomi a garin Damaturu.
Gwamnan yace, a iya sanin sa babu ko sisin kwabo da gwamnatin tarayya ta taba basu, illa sau daya kwamitin da gwamnatin Tarayyar ta kafa karkashin TY Dan Juma, wanda suka ziyarci Asibitin Damaturu inda suka bayar da gudunmawar Naira Miliyan 20, kuma yace har ya zuwa wannan lokaci ba a bada kudin duka ba.
Gwamnan ya kuma tabo batun tantance ma’aikata da akeyi a wasu kananan hukumomi biyar dake jihar Yoben, wanda yace hakan ya kama tilas ne don ganin yadda kowanne wata ana samun karuwar albashi maimakon a samu raguwa, ganin yadda Jama’a da dama ke yin ritaya wasu kuma su kan rasu amma albashi bai taba saukowa ba.
Tun shekara ta 2007 a cewar gwamnan basu dauki wani sabon ma’aikaci a kananan hukumomi ba, amma abin mamaki shine ana ta samun karuwar ma’aikata wanda har suka gano cewa, wasu ne ke sayar da takardun daukar aiki, kuma sun fara gano ire-iren mutanen.
Karancin kudi a jihar shine dalilin da yasa aka rage kudin da ake biyan matasa marasa aikin yi a jihar, wanda ada ana biyansu dubu 15 yanzu kuma ana biyansu dubu bakwai da dari biyar.
Don karin bayani.