Gwamnan wanda yanzu haka ya ziyarci kananan hukumomin da dama, ya ce a sakamakon lalacewar abubuwa yasa suka dauki matakin gudanar da rangadi a kananan hukumomin domin daukar matakin gyara na musamman.
Ya ce “abubuwa da dama sun lalace, shekara da shekaru ba a gyara, dan haka a matsayin gwamna tilas ne in gudanar da rangadi kamar yadda ake yi lokacin su Sardauna, amma a yanzu sai dai kawai a zauna a shalkwata cikin kwandisho, ana shan sanyi da ruwan shayi, sai lokacin zabe yayi sa’an nan a fara kewaya kananan hukumomi”
Ya kuma kara da cewa yanzu yana zagayawa da kuma ganawa da shugabannin kananan hukumomi domin ganewa idansa irin taimakon da suke bukata domin tallafa masu.
A karshen makonnan ne gwamnan ya ziyarci kananan hukumomin Borgu da Agwara, masu fama da matsalolin rashin kyawun hanya.
Malam Sani sa’idu mazaunin kauyen Shagunu, dake bakin kogin Neja, a karamar hukumar Borgu, ya ce matsalar rashin kyawon hanya da asibiti ya hadda rasuwar mata a kalla guda 50, sakamakon rashin hanyar da za a kaiga asibiti mafi kusa.
Gwamnan ya bayyana cewa yanzu haka suna wani shiri na musamman da zai bunkasa yankin domin janyo masu zuba jari.
Daga Minna, ga rahoton da Mustapha Nasiru Batsari, ya aiko mana.
Facebook Forum