Shugaba kungiyar a jihar Komred Samson Almuru, ya shedawa taron manema labarai a Yola fadar jihar cewa kungiyar ba ta anfana ko da sau guda ba daga tallafin da gwamnati tarayya ke rabawa jihohi.
Ya ce abin takaici shine duk da kasawar da gwamnati ta yi na ware mata wani kaso na kudin Faris kulob Naira miliyan tara da ta karba daga gwamnatin tarayya bara don rage bashin da ‘ya’yan kungiyar ke bin ta.’ko Naira biliyan daya da gwamna Muhammadu Umaru Jibirilla ya sanar ya ware don rage bashin hakkokin da tsoffin ma’aikatan ke bi makonni uku da suka gabata, har yanzu ba su gani a kasa ba’ inji Komred Samson Almuru.
Wadannan kalamai na shugaban kungiyar tsoffin ma’aikata ta kasa reshen jihar Adamawa ya tada hankalin mukarraban gwamna Jibirilla dalilin da ya sa kwamishinan kudi na jihar Alh, Sali Yunusa ya kira taron ‘yan jarida don ya baiwa tsoffin ma’aikata hakuri da alkawarin zasu biya hakkokinsu da zaran kudin Faris Kulob da shugaba Buhari ya alkawarta sun samu.
Kawo yanzu, akwai tsoffin ma’aikata da suka share sama da shekara shida suna yi wa kudaden sallamarsu jiran gawon shanu a jihar Adamawa.
Facebook Forum