Shalkwatar PDP, kuma karkashin mulkin Modu Shariff, ta bukaci kotun ta kori karar da cewar wadanda suka shigar da karar sojojin gona ne da wasu ke amfani da su.
Barrister Bashir Maidugu, shine mai ba jam’iyyar PDP, shawara ta fuskar shari’a, ya ce, “watsar da su kawai za a yi, domin haramtacciyar kungiya ce da suke kiran kansu bayan kuma kotu ta haramta hakan, idan ba sojojin gona bane ta yaya iyayen jam’iyya zasu nemi a yi sulhu amma mutanen makarfi ne kadai suka fito suka ce basu yarda ba”.
Zuwa yanzu dai kwamitin na makarfi bai shirya biyewa sunhun ba, Rufa’i Usman, dan PDP, sulhu ne da aka fara sauraron shari’ar a gabansa, ya bayyana cewa “mu bamu da wata shari’a, jam’iyyar PDP daya ce, da suka shigar da kara munje muji mai ke tafe da su, amma ina tabbatar maka da cewa bamu da shari’a da su.
Ko halarta a siyasance su Modu Shariff su rika ambaton wakilan Makarfi da cewa sojojin gona ne?, Dr Sadiq Abba malamin kimiyya ne kuma yayi Karin bayani akan wannan tambaya.
Domin Karin bayani, ga cikakken rahoton Nasiru Adamu Elhikaya, daga Abuja.
Facebook Forum