Shawarar Majalisar Dattawan na gaiyatar gwamnan babban Bankin Najeriya CBN, ya biyo bayan wani kudiri da dan Majalisar daga Jihar Filato ta Arewa, Sanata Istifanus Gyang Dung, ya gabatar a yayin zaman da suka yi kan umurnin da babban bankin ya bayar na dakatar da cibiyoyin hada hadar Kudi daga yin kasuwanci da kudaden cryptocurrency da dukan abin da suka shafe su.
Majalisar ta yi kira da a yi taka tsantsan a irin matakan da ake dauka musamman wadanda ke shafar harkokin kudade, saboda gudun kar ya shafi tattalin arzikin kasar da ya riga ya ruguje.
Duk da yake Majalisar ta yi amanna cewa cryptocurrency fasaha ce da ke canza yadda ake gudanar da kasuwanci, amma akwai abin da za a duba kamar yadda Sanata Istifanus Gyang Dung ya nuna cewa, ana iya amfani da cryptocurrency wajen sayan makamai ba tare da sanin wanda ya saya ba, kuma ana iya amfani da shi wajen sayan miyagun kwayoyi, har ila yau za a iya damfara wajen sace makudan kudade ta yanar gizo.
Saboda haka Sen Istifanus ya ce, Majalisa ta gayyaci gwamnan babban bankin ne domin ya yi wa majalisar bayanan tasirin kasuwancin cryptocurrecny ga kasa da yadda kuma masu yin kasuwancin za su amfana ko akasin haka.
Amma kwararre a fanin hada hadar hannun jari Kasimu Kurfi, ya ce matakin da bankin Najeriya ya dauka bai yi daidai ba, domin hanyar kasuwanci da cryptocurrency ita ce ta zamani da kasashen da suka ci gaba suke yi a yanzu.
Kurfi ya ce kamata ya yi babban bankin Najeriya ya yi dokoki da zai kare kasa da yadda ake mu'amala da kudaden.
Sai dai kwararre a fanin kundin tsarin mulkin kasa, Barista Ibrahim Bello, cewa ya yi matakin da babban bankin Najeriya ya dauka ya yi daidai, domin ya yi ne saboda kare mutuncin yan kasa kuma hurumin bankin ta yin haka.
Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.