Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele Ya Sake Kin Amsa Gayyatar Majalisar Wakilai


Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele

A karo na biyu jiya Talata gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele ya sake kin amsa gaiyatar Majalisar wakilai a bisa hujjar cewa bai dawo daga kasar waje ba.

Tun a ranar !5 ga wanan wata ne Majlalisar ta aike wa Emefiele da gayyata domin ya kara yi masu bayani akan manufar bankin kan sauya fasalin kudin kasar ciki har da takaita yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a asusun bankuna , amma zaman bai yiwu ba saboda an aike wa majalisar wasika cewa Emefiele ba ya kasar.

Haka a zaman na jiya talata ma, wasika ce mai dauke da sa hannun mataimakin gwamnan Babban Bankin kasar, Edward Adamu aka aika da ke cewa Emefiele bai dawo kasar ba har yanzu.

Wanan ya sa masanin harkokin diflomasiya da zamantakewan dan Adam kuma malami a Jami'ar Abuja, Dokta Farouk Bibi Farouk, ya yi nazari cewa dole ne Emefiele ya ji tsoron fuskantar Majalisa domin bai tuntubi Majalisar ba kafin ya dauki matakin da ya dauka akan sauya fasalin kudi da kuma yawan kudaden da mutum zai iya cirewa a asusun banki.

Farouk ya ce akwai badakalar da ake ta bincike akan sa saboda haka zai ji tsoron fuskantar Majalisar.

Shi kuwa kwararre a fanin tattalin arziki Ahmed Iliyasu Sardaunan Misau yana ganin ya kamata Majalisa ta ciza ta hura tunda an bada hujjar rashin zuwan Emefiele. Iliyasu ya ce ya kamata Majalisa ta yi wa Emefiele uzuri.

Dan majalisa mai wakiltan Birnin Kudu da Buji a Jihar Jigawa Magaji Da'u Aliyu wanda shi ne ya kawo kudurin gayyatar Emefiele a gaban majalisar ya yi duba da abin da doka ta tanada.

Magaji ya ce doka ta ba Emefiele dama ya nemi shawarar Majalisa kafin ya yi wani tsari da zai shafi kasa baki daya, amma bai taba zuwa wurin su ba.

Magaji yace yin haka ya karya dokar kasa da kuma dokar da ta kafa babban Bankin kasar..

Majalisar ta sake ba Emefiele dama ya bayyana a gaban ta a gobe alhamis, abin jira a gani shi ne ko hakan zai yiwu ko majalisa za ta yi masa uzuri.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
XS
SM
MD
LG